MAHDIN SHIA RAFIDAWA BAYAHUDE NE

MAHDIN SHIA RAFIDAWA BAYAHUDE NE:
Imamin yan Shia Rafidawa na goma sha biyu bayahude ne kamar yadda riwayoyi sukazo daga Imamai "wadanda basu kure [ma'asumai]."
Yazo a cikin littafin DALA'ILUL IMAMAH da littafin AL-TARA'IF cewã wai Annabi yace: "Mahadi daga diya na yake, fuskar sa tana walqiya, launin jikin sa na Larabawa ne, amma jikin sa na Yahudawa [Israielawa] ne...."
Yazo a cikin littafin AL-GHAIBA cewã Imam Abu Abdullah yace: "Idan Imam Mahadi yayi shela, zai kira Allah da sunan Sa na Abraniyyah [watau harshen Yahudawa]."
Kuma riwayoyi masu yawa sunzo a cikin littafin al-Kafi cewa idan Imam Mahadin su yazo zaiyi hukunci da littafin iyalan Annabi Dawud; watau bazaiyi aiki da Al-Qurani ba. Wannan na tabbatar muna da cewa tun daga farko Bayahude ne tushen addinin Shia.

لتحميل الملف pdf

تعليقات