شبهات وردود

A ADDININ SHIA RAFIDAWA ANA FIFITA MAGANAR IMAM AKAN AL-QURANI

A ADDININ SHIA RAFIDAWA ANA FIFITA MAGANAR IMAM AKAN AL-QURANI:

Yazo a cikin littafin al-Wilayatul Takwiniyyah lil-Nabi wal-A'immah [na Ayatullah al-Nammazi al-Shahroudi], shafi na 34 cewa: "Lalle tana yiwuwa a qaddamar da maganar Imam akan zahirin Al-Qurani. Kuma wannan maganar sananna ce, kuma tabbata a cikin Mazhabar Shia. Don haka zahirin Al-Qurani bashine hujja [abun nufi ba], ā'a maganar Imam ce kishiya, kuma yankan hujja akan zahirin Al-Qurani. Don haka haramun ne ayi riqo da zahirin Al-Qurani idan ya sabama maganar Imam."

Jama'a wannan shine addinin Shia Rafidawa, basu riqo da Al-Qurani da Sunnah saidai da maganganun da maqaryata suka tsara masu, wai shine bin Ahlul Bayt.


لتحميل الملف pdf

تعليقات