MISALAIN AYOYIN DA YAN SHIA KE DA'AWAR CEWA SAHABBAI SUN CANZA AL-QURANI
Allah سبحانه وتعالى Yace dangane da Al-Qurani:
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا بِالذِّكْرِ لَمَّا جَاءَهُمْ ۖ وَإِنَّهُ لَكِتَابٌ عَزِيزٌ
Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur´ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.
لَا يَأْتِيهِ الْبَاطِلُ مِنْ بَيْنِ يَدَيْهِ وَلَا مِنْ خَلْفِهِ ۖ تَنْزِيلٌ مِنْ حَكِيمٍ حَمِيدٍ
Ɓarna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde. (41:41-42)
Duk da tabbacin da Allah Ya bayar na kare saqonSa zuwa ga dukan mutane daga kowace irin barna ko canji, yan Shia sunyi Imani da cewa an cire wasu ayoyi daga cikin shi, an canza wasu kalmomi kuma an cire wasu kalmomin.
Ga kofe na littafin RISALATUL MUHKAM WAL-MUTASHABIH nan mun kawo maku don tabbatarwa. Kuma don Allah idan baka iya larabci ba, ka nemi wanda ya iya ya fassara maka.
لتحميل الملف pdf