ALLAH YA GAFARTA MA SAHABBAN MANZON ALLAH:
A koda yaushe yan Shia Rafidawa basuda abun la'ana da dariya sai Sahabban Manzon Allah. Daga cikin abunda suke zagin Sahabbai akai, gudun wasu daga cikin su daga fagen yaqi a ranar yaqin Uhudu. To wannan ba abun dariya bane domin Manzon Allah bai kushe wadanda suka yi gudu ba daga cikin su. Kuma an kashe dayawan su a ranar wurin kare shi, kamar yadda da yawan su sun jikata.
Allah Ya gafarta ma wadanda suka yi gudu a ranar, kuma ya karrama su domin Yasa wannan maganar a cikin Al-Qurani. Allah Ya ce:
"Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri." (Quran-3:155).
Yazo a cikin littafan Shia Rafidawa cewa Abu Abdullah yace; gudu a lokacin yaqi halat ne idan maqiya ko abokan gaba sun lunka Musulmi sau ukku.
Bugu da qari ga Mahadin su nan ya ranta cikin na kare ya boye. Yau yayi shekaru fiye da dubu da dari ukku yana boyo, domin kada a kashe shi. Wanda yayi Imani da irin wannan shugaba, shi ke yima wani dariya.
Allah Ya kiyashemu daga addinin Shia Rafidawa.
لتحميل الملف pdf