MENENE BANBANCI TSAKANIN YAN QADIYANIYYAH DA YAN SHIA RAFIDAWA DA AHLUS SUNNAH WAL-JAMAAH?
YAN QADIYANIYYAH: Suna da'awar cewa akwai wani Annabi bayan Manzon Allah [s.a.w], kuma Annabin nan nasu, ma'asumi ne [wanda baya kure], ana yi masa wahayi, kuma ana karbar addini daga gareshi.
YAN SHIA RAFIDAWA: Suna da'awar cewa akwai wasu Imamai [Shugabanni] goma sha biyu, kuma ma'asumai ne, kuma ana yi masu wahayi, [kuma dolene a karbi addini daga garesu].
AHLUS SUNNAH WAL-JAMAAH: Munyi Imani da cewa addinin Musulunci ya cika da Annabi Muhammad [s.a.w], kuma ya barmu akan hanya madaidaciya; daren ta kamar hasken Rana. Saboda haka bamu bukatar wani ma'asumi bayan sa. Allah سبحانه وتعالى Yace:
"...A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni´imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku..." [5:3]
Abun lura anan shine yan Shia Rafidawa sunyi Imani da wasu Annabawa goma sha biyu bayan Manzon Allah [s.a.w]. Amma maimakon su kirasu Annabawa sai suka kirasu Imamai [Shugabanni], wadanda Allah Ya zaba, kuma ma'asumai ne, kuma anayi masu wahayi, kuma wajibi ne a karbi addini daga garesu. MENENE BANBANCIN SU DA ANNABAWA?
لتحميل الملف pdf