AQIDAR SHI'A AKAN ASALIN SHI'ANCI:
Yan Shi'a sunyi Imani da cewa Shi'anci ya riga manzancin Annabi Muhammad [s.a.w] duniya domin duk Annabin da yazo kafin shi sai an kira shi zuwa ga Imani da shugabancin Ali. Yan Shi'a sun qirqiro tatsunniyoyi masu yawa domin tabbatar da wannan aqidar. Daga ciki sun labarto a cikin al-Kafi cewa Imam Abul Hasan yace: "An rubuta shugabancin Ali a cikin dukan littafan Annabawa, kuma Allah bai taba aiko wani Annabi ba face tareda Annabcin Muhammad da shugabancin Ali." [Al-Kafi, juzu'i na 1, shafi na 437].
📚 Ahlus Sunnah nayima Shia raddi da cewa: "Idan an ambaci shugabancin Ali a dukan littafan Annabawa, me yassa su kadai keda wannan riwayar kuma su kadai suka santa. Me yassa ba'a ambaci wannan shugabancin ba a cikin Al-Qurani tunda ya shafe dukan littafai kuma Allah Madaukakin Sarki Ya Kare shi daga canji?
لتحميل الملف pdf