Yan Shi'a sun ruwaito riwayoyi ingantattu a wurin su, cikin littafan su, masu cewa idan ya kasance babu Imam a cikin duniya wanda yake raye kuma yana rayuwa cikin mutane, suna ganin sa, kuma suna karbar addini da ilminsa a wurin sa, duniya zata ruguje da duk wanda ke cikin ta da dukan abunda ke cikin ta.
📚 Sai muka ce masu; a yanzu wane Imam ne ke zaune cikin duniya yana tareda mutane, kuma yana karantar dasu addini? Me yassa duniya bata ruguje ba, gashi kuwa yau fiyeda shekaru 1300 babu Imami ma'asumi a cikin mutane yana karantar dasu addini?
لتحميل الملف pdf